Maƙiyan Najeriya ne ke rikici da sunan zanga-zangar EndSars – Gwamnonin Arewa

 


Maƙiyan Najeriya ne ke rikici da sunan zanga-zangar EndSars – Gwamnonin Arewa


Ƙungiyar gwamnonin Arewa ta ce “maƙiyan Najeriya ne” da ke son sauya gwamnati ba ta hanyar zaɓe ba ke aikata ƙone-ƙone da sunan zanga-zangar EndSars.


Gwamnonin sun bayyana haka ne cikin wata sanarwar bayan taron gaggawa da suka gudanar a Jihar Kaduna ranar Alhamis ƙarƙashin jagorancin Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato.


Da yake karanta sanarwar, Simon Lalong ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su juya wa maƙiya baya ta hanyar mara wa gwamnatin Shugaba Buhari baya da dimokuraɗiyya baki ɗaya.


“Ƙungiyar ta yi takaici game da ayyukan wasu miyagu da ‘yan jagaliyar siyasa da ke ƙoƙarin sabauta ƙasa da kuma sauya gwamnati,” in ji sanarwar.


Ƙungiyar ta yanke shawarar faɗaɗa tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jihohinsu sannan ta buƙaci a kafa kwamitin shari’a domin ya binciki dukkanin kashe-kashe da lalata dukiya a lokacin zanga-zangar EndSars.”


Tuni Shugaba Buhari ya buƙaci masu zanga-zangar da su janye daga tituna.


Zanga-zangar ta fi ƙamari a jihohin kudancin Najeriya, inda wasu tsageru suka fasa gidajen yari a jihohin Edo da Legas tare da sakin fursunoni.

Leave a Reply

Your email address will not be published.