Dubban matasa sun yashe ɗakin ajiyar kayan abinci a Yolan Adamawa

 Dubban matasa sun yashe ɗakin ajiyar kayan abinci a Yolan Adamawa

Dubban matasa sun afka wa wurin ajiyar kayan abinci na gwamnatin Jihar Adamawa a birnin Yola yau Lahadi.


Fusatattun matasan sun karya ƙofar wurin ne da ke Kwanan Waya a wajen birnin Yola, inda ake ajiye da kayan tallafin annobar korona, a cewar rahoton jaridar Daily Trust.


Mutane da dama sun ɗauki kansu a bidiyo yayin da suke cikin ɗakunan ajiyar tare da sanya wa a shafukan zumunta, suna masu alfahari da ɗibar abin da suka ce haƙƙinsu ne.

Wani rukunin jami’an tsaro da aka tura wurin bai iya daƙile matasan ba daga jidar kayan Abincin.

Hatta babban titin Yola-Numan da ya haɗa Adamawa da Jihar Gombe an toshe shi saboda yawan masu kwasar kayan, in ji Daily Trust.

Domin siyan DATA Ta MTN da take yin wata daya 1GB Kan 350 Yi magana WhatsApp https://wa.me/c/2348122225296

Leave a Reply

Your email address will not be published.