Fusatattun matasa sun wawashe kayan sama da Milyan 2,00 a gidan sanata a Najeriya

 


 Fusatattun matasa sun wawashe kayan sama da Milyan 2,00 gidan sanata a Najeriya


Wasu fusatattun matasa sun afka gidan sanata mai wakiltar Mazaɓar Oyo ta Tsakiya, Teslim Folarin, inda suka wawashe kayayyaki.


Jaridar Premium Times ta ruwaito a ranar Asabar cewa matasan sun yi awon gaba da kayayyaki aƙalla 1,100 Wanda suka haɗa babura 350 da firji 400 da injinan niƙa da kayan Abinci da sauran kayayyaki na tallafa wa mutane a gidansa na Ƙaramar Hukumar Oluyole ta Jihar Oyo.

Yadda matasa suka wawashe kayan sama da Milyan 2,00 gidan sanata a Najeriya

Sai dai daga ƙarshe jami’an tsaro sun Sami nasarar cafke mutane bakwai daga ciki


Kazalika, jaridar ta ruwaito yadda aka wawashe gidan tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai Yusuff Lasun a Jihar Osun.


Haka nan wasu matasa sun yi yunƙurin shiga ginin Arts and Culture da ke Area 10 a Abuja domin ɗebe kayan abinci na tallafin annobar korona da suka ce an ajiye a ciki.


Leave a Reply

Your email address will not be published.