Gwamnatin Kaduna ta saka dokar hana fita na awa 24 Bayan Ɓata gari Sun daka wawa kan kayan Tallafin Korona


Gwamnatin Kaduna ta saka dokar hana fita na awa 24 Bayan Ɓata gari Sun daka 
wawa kan kayan tallafin abinci na korona


Kwamishinan Tsaro da Harkokin cikin Gida Samuel Aruwan ya bayyana cewa gwamnati ta saka dokar hana fita Sakamakon Ɓata gari Sun daka wawa kan kayan tallafin abinci na korona


Hakan ya biyo bayan ta’addancin da wasu ƴan iska a jihar suka yi ranar Asabar inda suka fasa dakin ajiyar kayan tallafin Korona suka yi awon gaba da su.


Aruwan ya ce ya zama dole a saka wannan doka domin kare mutane daga wadannan batagari da ke neman tada zaune tsaye a jihar.


Dalilin afkawa dakin ajiyar kayan tallafi na Covid-19 da wasu ‘Yan iskan gari suka yi a wasu sassan garin Kaduna, gwamnati ta saka dokar hana fita na awa 24 a kananan hukumomin Kaduna ta Kudu da wasu sassan karamar hukumar Chikun.


Yadda Ɓatagari suka farfasa dakin ajiyan abincin Tallafin Korona

Ƴan iskan gari tare da wasu mazauna unguwar sun far wa dakin ajiyar kayan tallafi na Covid-19 dake unguwar Barnawa, inda suka kwashe kayan dake ciki kaf, har da kofofi, da fitillu, kujeru da kwanukan rufin ginin.


Ba iya ɓatagarin ne suka far wa gidan ajiyan ba, har da mazauna unguwan duk sun fito sun kwashi rabonsu. Su ma sun bi sahun wadannan ƴan iska suna sace ajiyar gwamnatin.


Bayan haka sai wasu matasan daga unguwar Kakuri suka fara bi duk inda ake ajiye da wadannan kayan abinci suna farfasawa.


Gwamnatin jihar bata yi wata-wata ba sai ta saka dokar ta baci a yankunan da abin ya faru sannan aka aika da jami’an tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published.