An fasa rumbun ajiyar abinci da ke Gwagwalada a Abuja


 An fasa rumbun ajiyar abinci da ke Gwagwalada a Abuja


An fasa rumbun ɗakin ajiyar abinci na gwamnati da ke Gwagwalada a Abuja babban birnin Najeriya.


Cikin wadanda aka ga hotunansu suna kwasar kayan da akwai tsofaffin mutane da kuma matasa maza da mata da ke ikirarin kayan hakkokiinsu ne.


Mutane hudu ne suka faɗi yayin turmutsutsu kamar yadda rahotanni suka ruwaito, kuma masu kwasar kayan sun yi ta tsats tsallakawa ne ta shingen ginin da aka kafa domin kwaso ganima.


Kafofin yaɗa labaran Najeriya sun ruwaito cewa cikin kayan da aka wawashe akwai taliya da indomi da gishiri da shinkafa da sikari wandanda aka ce mallakar hukumomin birnin tarayyar ne.


Sojoji sun dira wurin da ake sace-sacen sai dai masu kwasar kayan ba su bar aikin da suke yi ba.


Ɓata gari sun Yashe Ɗakin ajiyar abinci a Abuja, sun kwashe komai. https://www.arewagist.com.ng/2020/10/gari-sun-yashe-akin-ajiyar-abinci-abuja.html


Tuni dai Ministan babban birnn tarayya, Abuja, Malam Muhammad Bello, ya bayar da umarnin a kama ma su barnar da suka balle babban shagon kayan abinci da ke unguwar Gwagwalada tare da gurfanar da su a gaban kotu.


Ministan ya bayar da wannan umarni ne yayin taron gaggawa da ya gudanar da shugabannin hukumomin tsaro na Abuja a ranar Litinin.


Ministan ya bukaci mabarnatan su gaggauta dawo da kayan da suka kwashe a yayin da yake sanar da cewa an baza jami’an tsaro domin kare sauran manyan shaguna da ke rukunin masana’antu da ke Idu.


A cewar Ministan, abinda yake faruwa yanzu ba zanga-zangar ENDSARS bace, sata ce da ‘yan iskan gari ke yi.


A nata bangaren, karamar ministar Abuja, Dakta Ramatu Aliyu, ta yi Alla-wadai da abinda ya faru cikin kakkausar murya


Ministar ta ce babu wata kasa da zata rayu ba tare da ma’adanai na abinci ba irin wadanda yanzu mabarnata ke ballewa suna kwashe abincin ciki.


Domin siyan DATA Ta MTN da take yin wata daya 1GB Kan 350 Yi magana ta WhatsApp https://wa.me/c/2348122225296

Leave a Reply

Your email address will not be published.