Matasa sun ɓalle ma’adanar kayayyakin tallafin Abinci na korona


Matasa sun ɓalle ma’adanar kayayyakin tallafin Abinci na korona

Lamarin ya faru a jihar Kogi a ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoban 2020


– Matasan sun gano inda aka adana tallafin ba tare da an raba musu ba


Mazauna jihar Kogi da ke Arewacin Najeriya sun fasa ma’adanar kayan tallafin COVID-19 da aka bai wa jihar.


Kamar kowacce jihar, sun kwashi iyakar kayan da za su iya kwasa sannan suka yi awon gaba da su, shafin Linda Ikeji ya wallafa.


Balle wuraren adana tallafin korona a jihohi ya fara daga yankin kudancin kasar nan bayan zanga-zangar EndSARS.


Lamarin ya cigaba da shigowa jihohin arewa inda fusatattun matasa ke nemo ma’adanar kayan rage radadin.


Sakamakon yawaitar ɓalle ma’adanar kayayyakin tallafin, gwamnatocin jihohi daban-daban sun saka dokar ta-ɓaci.


A wani labari na daban, bata-gari sun cigaba da yadda suka ga dama da dukiyoyin gwamnati da na al’umma sakamakon barkewar rikicin zanga-zangar EndSARS, Daily Trust ta wallafa.


A jihar Benin, Anambra, Edo, Kaduna, Filato, Cross River Adamawa da Ekiti, matasa sun yi ta shiga ma’adanai, inda aka ajiye kayan tallafin COVID-19, wadanda ya kamata a raba wa talakawa, suna awon gaba da su.


Manema labarai sun tattaro bayanai a kan yadda mutane 5 suka rasa rayukansu a jihar Edo, 5 a jihar Taraba da kuma wani mutum a Anambra, duk sakamakon kwasar kayan abincin.


Wasu matasa sun kwashi buhunan kayan abinci bayan balle kofofin ma’adanar kayan tallafin COVID-19 na gwamnatin jihar Filato dake Jos a ranar Asabar.


Domin siyan DATA Ta MTN da take yin wata daya 1GB Kan 350 Yi magana ta WhatsApp https://wa.me/c/2348122225296

Leave a Reply

Your email address will not be published.