Pogba ya musanta labarin cewa ya daina buga wa Faransa wasa


 
Dan wasan Manchester United Paul Pogba ya musanta labarin da ke cewa ya daina buga wa ƙasar Faransa wasa saboda addininsa na Musulunci. 


Pogba ya ce wata kafar yada labarai ce ta ƙirƙiri labarin ƙanzon kuregen kuma ya sha alwashin kai ƙarar da wadanda suke da hannu a gaban kotu, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Instagram.


Dan wasan mai shekaru 27 ya wakilci kasar Faransa a wasanni 72 inda ya tallafa mata wajen lashe gasar cin kofin duniya na shekarar 2018, kuma yana kan gaba wajen yan wasan da kasar ke alfahari dasu .


Domin siyan DATA Ta MTN da take yin wata daya 1GB Kan 350 Yi magana ta WhatsApp https://wa.me/c/2348122225296


Ƙasashen Musulmi sun fara ƙaurace wa kayan Faransa Wanda ayanzu an fara cire kayan da Faransa ke samarwa a wasu shaguna da ke Kuwait da Jordan da kuma Qatar


Shugabannin siyasa a Turkiyya da Pakistan sun zargi Macron da rashin girmama ƴancin addini da kuma shiga hakkin Musulmi a Faransa.


Ko a ranar Lahadi shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya shawarci Mr Macron da yaje ayi masa gwajin kwakwalwa kan yadda yake kallon addinin musulunci.


Shi ma shugaban Pakistan Imran Khan ya zargi Macron da faɗa da addinin Musulunci kuma ya nuna ƙarara cewa ya jahilci wane irin addini ne.


Batun ƙaurace wa kayan Faransa shi ne maudu’i na biyu da yafi jan hankali a Saudiyya, ƙasa mafi ƙarfin tattalin arziki a Gabas Ta Tsakiya.

Ɓata gari sun Yashe Ɗakin ajiyar abinci a Abuja, sun kwashe komai. https://www.arewagist.com.ng/2020/10/gari-sun-yashe-akin-ajiyar-abinci-abuja.html

Leave a Reply

Your email address will not be published.