An bar iyaye cikin duhu kan batun buɗe makarantu a Najeriya - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Saturday, October 3, 2020

An bar iyaye cikin duhu kan batun buɗe makarantu a NajeriyaAn bar iyaye cikin duhu kan batun buɗe makarantun Najeriya


Sanarwar buɗe makarantun Najeriya ta faranta ran iyaye amma kuma gwamnati ta bar su cikin duhu kan makomar karatun ƴaƴansu.


A ranar Juma'a ne gwamnatin Najeriya ta sanar da bayar da umurnin buɗe dukkanin makarantu a ƙasar bayan kusan wata shida suna rufe tun a watan Maris saboda annobar korona.


Ministan Ilimi Adamu Adamu wanda ya bayar da sanarwar, ya ce za a buɗe makarantun sakandare na gwamnatin tarayya ranar 12 ga watan Oktoba, yayin da makarantun gwamnati a jihohi da makarantu masu zaman kansu za su fitar da nasu jadawalin buɗe makarantun.


Ministan ilimin ya ce za a buɗe makarantun ne saboda raguwar yaɗuwar annobar korona a Najeriya.


Sai dai a sanarwar, gwamnatin Najeriya ba ta bayyana yadda tsarin karatun zai kasance ba musamman zangon karatun da za a koma.


Shin wane zangon karatu za a koma?

Za a ci gaba ne daga zangon da aka tsaya? Ko wata sabuwar shekarar karatu za a soma? 

Tambayoyin da wasu iyaye ke yi kenan kan makomar karatun ƴaƴansu.

 

Domin siyan DATA Ta MTN 1GIG akan 350 Yi magana ta WhatsApp 08122225296


Wasu ƙasashen da suka buɗe makarantunsu sun amince ɗalibai su tsallaka zuwa aji na gaba, maimakon ci gaba daga inda aka tsaya, duba da yadda shekarar karatun ke dab da ƙarewa.


Me iyaye ke cewa?

Duk da cewa wasu iyaye sun yi murna da sanar da ranar da ƴaƴansu za su koma makaranta, wasu kuma na ganin an makara.


Kamar Kabiru Marmara wani uba da ke da yara a makaranta, ya shaida wa BBC cewa "tuntuni ya kamata gwamnati ta buɗe makarantu kamar yadda aka buɗe kasuwanni da wuraren ibada da kuma amincewa da tarukan ƴan siyasa.


 Wasu iyayen, annobar korona ta yi wa karatun ƴaƴansu illa, amma duk da haka suna farin ciki da jin labarin komawar ƴaƴansu makaranta.


An garzaya da shugaban Amurka zuwa asibitin ne bayan ya kamu da cutar korona

https://www.arewagist.com.ng/2020/10/an-garzaya-da-shugaban-amurka-zuwa.html?m=1


Wasu iyayen kuma kamar wata baiwar Allah, ta ce kamata yayi gwamnati ta bari sai watan Janairu ɗalibai su koma karatu, saboda yanzu ko sun koma ƴan kwanaki za suyi kuma a tafi hutun kirsimeti.


"Yanzu za a sa iyaye su biya kuɗin makaranta a wannan yanayin da ake ciki, ya kamata gwamnati tayi tunani."


Amma ga ɗalibai kamar na sakandare suna ganin koma wa makaranta wani muhimmin labari ne, saboda watannin da suka shafe suna zaman gida ba karatu.


Me sanarwar gwamnati ke cewa?

Bayan sanar da ranar buɗe makarantun Najeriya, ministan iilimi Adamu Adamu ya ba iyaye haƙuri kan tsawon lokacin da aka ɗauka makarantun na rufe, inda yana mai cewa an yi hakan ne da kyakkyawar niyyar daƙile bazuwar annobar korona wacce a yanzu a cewarsa, "an shawo kanta a Najeriya."


Ministan ya ce jihohi da makarantu masu zaman kansu za su iya buɗe makarantunsu a duk lokacin da suka ga dama.


Jihohi da yawa irinsu Legas da Oyo da Kano da Enugu tuni suka sanar da ranakun komawar ɗalibai.


Ba abinda hankali zai dauka bane, man fetir yafi arha a Najeriya kan Saudiyya

https://www.arewagist.com.ng/2020/10/muhimman-jawaban-buhari-na-cikar.html


Sharuɗɗan da gwamnati ta gindaya

Gwamnatin Najeriya ta ce dole ɗalibai da malamai su wanke hannu da sanya takunkumi.


Daga cikin sharuɗɗan da gwamnatin tarayya ta gindaya wa makarantu sun haɗa da:


 Tabbatar da bayar da tazara


Gudanar da bincike da yin nazari kan matsalolin da za su iya haifar da yaɗuwar cutar


Tabbatar da tsaftar muhalli da tanadin ruwa da sinadarin wanke hannu.


Tilasta amfani da takunkumi.


Duba yanayin zafin jikin ɗalibai da kuma duk baƙon da ya kawo ziyara makaranta.


Kafa kwamitin da ya ƙunshi malamai da ɗalibai da zai kula da kiyaye sharuɗɗan da aka gindaya na daƙile bazuwar korona.


Ministan ilimin Najeriya Ml Adamu Adamu ya yi gargadin cewa dole makarantu su tabbatar da sun bi dukkanin dokokin da aka gindaya na kariya daga annobar korona kafin bude makarantun, inda yace za a rufe duk makarantar da aka kama ta saɓa ka'idojin.


El Rufa'i ya soke zaɓen farko na masu zaɓen sabon sarkin Zazzau

https://www.arewagist.com.ng/2020/09/yunurin-farko-na-naa-sabon-sarkin.html

No comments:

Post a Comment