Zafafan Hotunan Rahama Sadau da sun janyo ce-ce-ku-ce


Zafafan Hotunan Rahama Sadau sun janyo ce-ce-ku-ce

Tauraruwar Kannywood Rahama Sadau ta ce sam “ba da yawunta ba” aka dinga kalaman ɓatancin da wasu suka riƙa yi biyo bayan wallafa wasu hotuna da tayi a shafukan sada zumunta.


Kalaman na tauraruwar fina-finan Kannywood da Nollywood na zuwa bayan wasu sun yi ta amfani da maud’in #AssistantAllah a Twitter da zummar kare ta daga sukar da wasu ke yi mata kan bayyana jikinta a sabbin hotunan da ta saka.


Da yawa daga masu sukarta na alaƙanta abin da tayi rashin dacewa da shigar Musulmi ko kuma Hausawa, abin da ya jawo wadanda ba Musulmi ba yin kalaman ɓatanci ga addinin da kuma Allah.

“Ina Allah-wadai da duk wani wulaƙanci ga addinina da Annabi game da waɗancan hotuna,” in ji Rahama cikin wasu jerin sakonni da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Litinin.


“Ya kamata miyagu su gane tsarin rayuwar mutane da kuma girmama addininsu.”


Tun safiyar Litinin sunan Rahama Sadau ke yawo a Twitter, inda aka ambace shi sau fiye da 10,000.


Hotunan da ta tauraruwar ta saka sun ja hankalin masu bibiyarta da kuma masu amfani da Twitter musamman daga arewacin Najeriya.


Duk da wasu na caccakar jarumar game da hotunan da ta wallafa, wasu kuma kare ta suka yi.

Da yawa suna nuna sha’awarsu da hotunan, yayin da wasu kuma suke nuna rashin dacewar hotunan a kafafen sada sumunta.


Rabuwar kan da aka samu tsakanin masu amfani da shafin, ba wani bakon abu bane sai dai a wannan karon ya dauki sabon salo.


Mafi yawan wadanda suka fito daga yankin kudancin Najeriya na yabon hotunan, yayin da waɗanda suka fito daga arewaci ke suka.


Amma ba abin mamaki bane wannan, saboda hakan na da alaka da al’adun yankunan biyu da suka sha ban-ban.


Sai dai mata da dama a Twitter sun kare jarumar suna cewa ba suga munin hotunan ba.

Abin da ƴan Twitter ke cewa:

Daya daga cikin wadanda suka nuna goyon bayansu ita ce Mrswalida, wadda tace ki baɗa musu yaji Rahama Sadau.


@Abdousalga ya ce sun nuna damuwa da ita saboda fitacciya ce kuma ta kasance wadda wasu ke kwaikwayo da ita


@_hafsat_paki ta ce kayan birge ta suka yi, a ba ta kwancen kayan.


Martanin Rahama

Da misalin ƙarfe biyar na yammacin ranar da ta wallafa hotunan ne Rahama Sadau ta wallafa wani saƙo a Tuwita ɗinta da ke cewa: ”Salam, abin takaici ne da ɓacin rai na tashi naga wasu jerin saƙonnin da ban yi tsammani ba, kan wasu hotuna da na wallafa da ba za su cutar da kowa ba.


”A matsayina ta ƴar adam na yi dariya kan wasu saƙonnin, na ji haushin wasu sannan na yi watsi da wasu.”


Sai dai jarumar ta ce babban abin takaicinta shi ne yadda yadda wasu suka dinga wasa da Allah da yin kalamai marasa daɗi kan Annabi SAW da addinin Musulunci.


”Ina mai matuƙar neman afuwa kan abubuwan da suka farun da ban tsammace su ba, waɗanda suka jawo lamarin da ba a san zai faru ba kuma ina nadamar faruwarsa.”


Rahama ta kuma yi godiya ga waɗanda ta ce sun nuna damuwarsu kan abin da ya farun har ma suka aike mata saƙonni da ma masu kiran ta a waya.


Sannan a ƙafrshe ta ja ”hankalin fitattun masu amfani da shafukan intanet da ma duk wanda ke ganin wannan abu a matsayin damar da zan yi tashe, to ba na muku fatan abin da kuka yi min fata.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.