Shin Inksnation za su Sami bayanan ATM dinka Idan ka biya kuɗin Verification ?


Mutane da dama basu san online payment gateways ba, Kawai suna tunanin idan suka ga ansaka Api na payment gateways a website, suna ganin kamar website din ake sakawa lambobin ATM card dinsu.


To ba haka abin yake ba, idan kaga an saka hanyar Biyan kuɗi a website to se ka kula kaga wane payment gateway aka saka.


Dalili kuwa shine bayanan ATM card dinka, wannan payment gateways dinne suka sansu, ba wai company ko website da sukace ka biya ba.


Yanzu misali mu dauki inksnation za kaga suna aikine da payment gateway na Paystack da flutter web, to kaga sune suka san details dinka na Atm ba InksNation ba, kuma sun Sami sahhalewa daga Babban bankin ƙasa CBN.


To amma kuma ai ni banga ankaini website din paystack ba, akan na inksnation na  ganni.?

Ranka ya dade ai yanxu anci gaba a duniyar internet, mu awajenmu ba bakon abu bane, amma ka tambayi web developers zasu baka darasi akai.


To Amma kuma naji sunce wai dole se ansaka BVN anya kuwa ba so suke su dauke mun kudina ba ta cikin BVN dina ba?

Yallabai ba bu alaka tsakanin fitar da kudi ta hanyar BVN.


Bvn ai KYC ne bayanai ne naka aciki, amma ina baka shawarar katambayi Masana banki dan kafi nutsuwa.


Kai anya kuwa gaskiya nifa inajin tsoro kar naje su kwashen kudadena?

Yallabai ba lallai ba dole inbaka nutsu da InksNation baza a tilastaka maka ba sai ka saka ba, Kamar yadda lokacin da kashigo ba wanda ya tilasta maka.

Leave a Reply

Your email address will not be published.