MENENE BLOCKCHAIN ?

MENENE BLOCKCHAIN ? 

Blockchain wani tsararren al’amari ne da zamani yazo dashi wanda aka sarrafashi ta hanyar duk mutumin da ya shiga cikinsa to ya shiga kenan, sunan nashi watau blockchain idan ka lura kalmomine guda biyu Block da Chain.

Kowa yasan menene Block ma’ana dai block na nufin BULO da ake yin gini dashi, chain kuma kowa yasan ita ce SARKA da mata ke daurawa a wuyansu. 

To amma shi wannan blockchain na Internet ba yana nufin wadancan abubuwan na sama ba, shi wannan kamar gini ne da aka tsara BULO din wannan gini daki bayan daki watau daya bayan daya kenan, kamar yadda ake yin Ginin gida watau bulo a jere har a gama wannan gida, to haka shima wannan blockchain na internet yake, ma’ana duk wanda ya shiga wannan gini na internet to ya shiga kenan, sannan abun na tafiyane in chain, idan na farko ya shigo to na biyu zaibi bayansa na uku haka na hudu haka har na biyar koma nawa ne, haka zaku hadu ku tada wannnan gini na internet har ya zama gida wanda zai zamto abu mai amfani a gareku.

 Kenan idan ka shiga cikin jerin wannan gini na internet kamar ka bayar da tallafi ne wanda daga bisani zai amfaneka shi wannan tallafi da ka bayar, sannan idan ka shiga cikin gini yana tattare da mukullin sirri wanda babu wanda ya sanshi ko kuma ya iya buda maka wannan sirri, watau abune mai matukar sirri. To karkashin wannan ne sai aka samar da wasu kudade da ake kira CRYPTOCURRENCIES.

ME NENE CRYPTOCURRENCIES ?

CRYPTOCURRENCIES/DIGITAL CURRENCIES kudade ne na zamani da ake kirkira a Kan internet, wanda masana na’ura mai kwakwalwa ke kirkirar wannan kudi. 

Kudaden ba a taɓa su a zahiri sai dai akanyi sample din yadda suke ko kalar yadda kudin suke, sannan kudaden silalla ne idan da zaka gansu a zahiri, shi isa ake kiran su COINS. 

Akan kirkiri wadannan kuɗaɗe don a rage amfani da yawo da takarda na kudade a hannun al’umma, sannan kuma akan yisu ne da nufin ayi amfani dasu ta fuskar saye da sayarwa ko a ajiye a matsatin kadara idan suka ƙara daraja a siyar. 

Su wadannan kudade akanyi amfani dasu da dama a wasu kasashe da suka cigaba, wasuma sukan mayar dasu kudaden da za a iya siyayya dasu a fadin kasar tasu, ma’ana sun mayar dasu LEGAL TENDER. 

Sannan su wannan kudi da kowace kasa zata rungumesu to da ansamu tsaikon barna da yawa da suka shafi sata, fashi da makami,kidnapping ace sai anbada kudin fansa, sannan kudade ne masu tsaro sosai da ba wani mahalukin da ya isa ya gansu ballantana ya taɓa su. 

Wannan kudi sun hada da su irin : 

BITCOIN 

ETHERIUM 

LITECOIN 

TRON 

CMDX 

SMARTKEY 

XRP COIN 

PINKOIN  etc.

Wadannan kudade wasu akan samesu ta hanyar idan kayi register ka gayyato wani shima yayi sai a biyaka, wasu kuma zaka sayesu a matsayin kadara ka aje idan sukayi tsada ka fitar ka sayar, domin suma sukanyi daraja ne lokacin da mutane suka bukacesu sosai wanda ake kira da DEMAND AND SUPPLY, yanayin yadda mutane suka bukaci amfani dasu yanayin darajarsu. Akwai wurare da yawa da ake sayar dasu kamar irin su :

BINANCE MARKET 

TOKEN POCKET 

Kucoin

Luno da sauransu

Leave a Reply

Your email address will not be published.