Ma’anar kalmomin Crypto da ya kamata kasani

 

Ana cewa “idan kana so mutane su fahimce ka to kayi Musu magana da Yaren su” haka ma “idan zaka Fahimci Crypto to Ka fahimci/koyi Yaren Crypto” 
 
A Crypto akwai Kalmomi da salon maganganu da inkiyoyi da ake amfani dasu wajen mu’amala da kuma aiwatar da Kasuwar sa.
 
 Wadannan kalmomi suna da matukar tasiri da kuma amfani ga wanda duk yake a cikin Crypto, domin sune yaren da ake magana dasu, idan ya zamana mutum baya gane su to zai iya fuskantar samun matsala wajen rashin sanin hatta inda kasuwa take yi.
 
1. All Time High (ATH):Mafi kololuwar farashin da coin ya taba kaiwa. Ana rubuta ta kamar haka Bitcoins ATH: $64K.
 
2. All Time Low (ATL): Ana Nufin mafi munin karyewar farashin da Coin Yayi a Kasuwa. Ana rubuta ta ne kamar haka, Ripple XRP ATL: $0.5
 
3. Bag:Ana amfani da ita ne Wajen fadar cewa mutum ya mallaki adadi mai yawa na wani coin. 
 
4. Buy The Fucking Dip (BTFD): Ana amfani da ita wajen fitar da Analyst na Coin ma’ana jama’a su sayi mafi saukar farashin Coin din. Misali ka sayi Doge BTFD $0.23
 
5. Alternative Coin (Altcoin): Ana Nufin dukkanin wani coin da ba Bitcoins ba. 
 
 
6. Shitcoins: Ana nufin Coin din da baida da Daraja, Idan ma yayi to ta wani gajeren lokaci ce.
 
7. Bear/Bearish: Ana Nufin lokacin da Coin yake faduwa kasa a farashin sa. Za’a iya cewa WIN ma yanzu yayi Bearish.
 
8. Bull/Bullish: Ana Nufin yanayin da Coin yake haw-hawa a Farashin sa. 
 
9. Dump: Ana amfani da ita Wajen fadar an sayar da wani Coin Mai yawan gaske.
 
10. Pump: Ana amfani da ita wajen fadar cewa Coin kaza yayi mugun tashi, musamman idan aka samu wani ko wasu masu kudi suka zuba makudan kudade acikin sa. Wanda hakan shi zai saka ya tashi.
 
 
11. Gas fee/Gas: Sune kuɗin da ake biya Wajen Transaction, wato charges na transactions.
 
12. Transaction: Ana Nufin shige da ficen kuɗi ta hanyar siye ko sayarwa.
 
13. Stablecoins: Sune Coins din da ake hadashi da kudin dala domin a tsayar musa da farashi kuma a hanashi yawan bazuwa a kasuwa. Misali USDT, BUSD d.s.s
 
14. Whitepaper: Wani Kundi ne daya  yake ɗauke da Bayanin coin da dalilin kirkiro sa da kuma abinda ake so a cimma manufa akansa.
 
15. Fiat: Kudin da ke karkarshin ikon gwamnati kuma ta yarda ayi cinikayya dasu. Misali Dollar, Naira, Euro d.s.s
 
 
16. Tokenomics: Kalmomi ne guda biyu Token + Economics. Fasahar da ake amfani da ita wajen gane yawan coins din da za’a fitar da kuma yawan masu Buƙatar sa.
 
17. Airdrop: Tsarin da ake amfani dashi Wajen rabawa ko Tallatawa jama’a Tokens ko Coins Kyauta domin su fara Ajiye shi.
 
18. Cryptography: Hanyar da ake amfani da ita wajen kirkiran Coin, da Kuma gudanar da shi akan na’urorin kwamfuyutoci domin tabbatar da tsaro a kansa.
 
19. Wallet: Jaka ko lalitar da Mutum yake adana Coins dinsa a ciki. Misali  Trust Wallet, Safepal Atomic wallet Metamask d.s.s
20. Decentralize Finance (DEFI): Tsarin Kasuwancin Crypto da ya bada yancin gashin kai na cinikayya ba tareda wani ya shiga ciki ba.
 
 
21. Centralized Finance (CEFI): Tsarin Farko da aka fara gudanar da Kasuwancin Crypto kafin (DEFI), Wannan tsarin Kasuwancin Crypto ya kunshi amfani da kasuwanni/Exchangers wajen Kasuwancin. Maslan Binance, Kucoin FTX d.s.s
23. Initial Coin Offering (ICO): Shine tsarin da ake siyar da coins ga wani adadin mutane domin a fara samun kuɗin da za’a yi amfani dasu wajen ɗaukar nauyin project din. 
 
24. Initial Dex Offering (IDO): Shine Dora Coin na akan kasuwar Decentralized Exchange (DEX).
 
25. HODL: Wato Kalmar kodumo ce wannan ainihin ta haka take “HOLD” ma’ana Riƙewa. Ana amfani da ita idan mutum ya sayi Coin Kuma zai ajiye zuwa wani lokaci da idan ya tashi zai sayar.
 
 
26. Fear of missing Out (FOMO): Wannan kalmar ana amfani da ita Wajen bayyana yanayin da mutum yake sauri ya sayi coin sakamakon wani tashi da yayi a baya yanzu ya sauka to sai kaga Mutum nata kokarin sai ya mallaka domin kada nan gaba idan romon yazo ya wuce shi.
 
To a wannan hakan yana kai mutane da dama zuwa ga yin asara sakamakon wannan saurin da zumudin domin kuwa mutum zai saya ne “sama ta ka” bai san halin Coin din a Kasuwa ba.
 
27. Not Gonna make it (NGMI):Sara Ce da masana Crypto Suke Amfani da ita wajen faɗin cewa wane zai rasa Riba mai yawa a wani coin.
 
28. Erc-20: dukkanin wani token da aka gina shi akan network na Ethereum to sunan wannan token din Erc-20 Token
 
29. Bep-20: Dukkanin token din da aka ƙirƙire shi akan Binance Smart Chain (BSC) to Sunan sa Bep-20 (BSC) Token.
 
30. Trc-20: Dukkanin token din da aka ɗora shi akan Tron Network to Sunan sa Trc-20 Token.
 
 
31. Non Fungeble Tokens (NFT): Su wadannan wasu Tokens ne da suke baiwa mutum damar saye ko sayar da kadara kamar, Zane, sauti na muryoyi, dama katin shiga kasuwar Crypto ta hanyar amfani da Smart contract. Suma NFTs na iya zama kamar ko wacce kadara da kana iya sayen ta da nufin idan ta kara daraja ma siyar.
 
32. Rekt: A ta taccen turanci kuma “Wrecked” shine mutumin da ya zuba kudi Sosai a Crypto Kuma Yayi asarar su. Allah Ya kiyaye mu daga asara.
 
33. Not Financial Advice (NFA): wannan wani tag ne da Masanan kasuwar ko kuma masu Bibiyar yanda ake gudanar da Ita yau da kullum, suke anfani da ita a karshen rubuce-rubucen su da suke wallafawa a Kafafen watsa labarai.
Ana fadar hakan ne domin tabbatar da cewa wannan alkaluman da aka baka bawai suna kasancewa 100% dai-dai bane, domin kasuwar tana iya canzawa saɓanin yanda ka sani ko ka karanta, to yanada Kyau shi mai karanta wannan alkaluman ya san haka.
 
29. Do Your Own Research (DYOR): kayi Bincike ka tabbatar da sahihancin  coin da kanka. 
 
Ana amfani da wannan wajen matsawa sabbin shiga Crypto da suma suyi Bincike kafin su zuba kudin su a wani coins ko Tokens domin su rika sanin kasuwa kafin su shiga ciki.
 
30. Market Cap (MC): yawan adadin kudin Coin Dake cikin kasuwa. Ana amfani da formula kamar haka wajen lissafa shi.
Mcap = Current Price x Circulating supply
 
Maslan. Idan Coin yana da Circulating supply guda miliyan 10 kuma farashin kowanne daya aciki $1 to Market cap dinsa zai kasance miliyan 10.
Mcap = 10,000,000 x $1
Mcap = $10,000,000
 
 
31. Burned: wato konewa ko a Hausance, ana amfani da ita idan za’a bayyana wani sashen Coin da ya zamana baya aiki an kone shi kenan. 
 
Misali za muce zuwa yanzu Freecoin ya kone sama da Coin Biliyan talatin kenan cikin zagaye uku na fara sayar da shi a kasuwa.
 
32. Use Case: ana amfani da wannan wajen nuna abubuwan da za a iya amfani da coin.
33. Fundamental Analysis (FA):Shine irin tsarin Binciken da akeyi idan masana sunce maka “DYOR”.
Wato bincike ne da ya kunshi duba use Cases na coin, Adadin mutanen da suka mallakeshi da Team din da suke aikin sa ko kuma suka samar dashi.
 
33. Swapping: musayar Coin Zuwa Tokens, bani gishiri na baka manda.
 
 Mutum yanada BNB sai ya sayi CAKE a Pancakeswape to Zamu ce yayi swapping din BNB dinsa zuwa CAKE.
 
34. Circulating Supply Coin din da yake a cikin Kasuwa wanda ake juyawa ana saye da sayarwa, wasu coins din ana kulle su, wani kuma a ɓoye ya zama reserve, wani kuma ayi burning nashi to duk wanda ya fado wannan kashin ba za’a ganshi a kasuwa ba. Ma’ana baya cikin Circulating supply.
 
35. Decentralize Application (dApps): Manhajoji ne na browser da ake amfani dasu wajen saye da sayarwa na Tokens ko Coins musamman wajen wajen swapping.
 
36. Dust Transaction: Wato idan akayi wa Manhajar Transaction nauyi na masu Transaction da yawa wanda hakan sai yasa duk abubuwan su rika tafiyar wahainiya to wannan shi ake kira da Dust Transaction.
 
37. Whale: Mutumin da yake da makudan kudaden da zai iya juya akalar kasuwa. Misali Elon musk 
 
38. FUDster: mutumin da yake yada labarai na kanzon kurege, yake cusawa jama’a tsaro da shakku akan wani coins ko Tokens.
 
39. Moon:Inkiyar numa cewa wani coin zai tashi sosai. 
 
40. Lambo: Lamborghini ana amfani da wannan kalmar mai Sunan wani kamfanin mota wajen nuna cewa coin din nan zai kawo kudi ko kuma wane ya samu kudade sosai dashi.
 
 
41. Cryptocurrency: Kudaden kwandaloli na internet
 
42. Blockchain: Wato fasahar dake dauke da Cryptocurrency gaba dayan ta.
 
43. Paper Hand: Shine wanda ko yaya Coin ya sauka sai su sayar.
 
44. Diamond Hand: Shine Wanda yake Hakuri da Coin din dake hannun sa
 
45. Private keys: wasu kalmomi ne da ake amfani da su wajen shiga lalitar ajiye coins wato Wallet.
Akiyaye wajen Adanawa yanda ya kamata
 
46. Farming: Noma kenan a Hausance, to a Crypto to ma anayin noma, mutum ya ajiye coins dinsa ana juyawa yana samun Riba.
 
47. Digital wallet: wallet din da ake ajiye coin na Crypto walau ta waya kota kwamfuyuta.
 
48. Degen/Degen Trader: shine mutumin da yake yawan Bibiyar projects domin a Tunani sa anan kadai zai kwashe
 
 
49. ESCROW: Wadansu kamfanonin da suke aiwatar da Transaction na Tokens
 
50. Exchange: shine Inda mutane suke zuwa/shiga domin aiwatar da saye da sayarwa na coins. Mai gudanar da wannan aikin kuma sunan sa Exchanger.
 
Wadannan kalmomi bawai su kenan ba akwai ire-iren su masu yawa, wadanda ba wadannan ba, yanada kyau kayi kokari inda hali ka sansu domin zasu taimaka maka sosai.
 
1. HODL The act of holding a coin for the long term instead of selling it. Made famous by this epic post.

2. Altcoin Every cryptocurrency other than bitcoin

3. FOMO Fear of missing out. This happens when a coin is rising in value and you’re considering buying at a high price even though you might be too late

4. JOMO Joy of missing out. This happens when you dodged a bullet and are happy you didn’t buy a coin

5. Moon Where everyone wants their coin to go, up and into outer space

 

6. Bag Holder Someone who is holding a lot of coins in the hopes that it will go up in the future

7. Shitcoin A worthless and dead coin with no real value

8. Dumping Downward price movement or a decision to sell a coin

9. DYOR Do your own research

10. FUD Fear, uncertainty and doubt

 

11. Whale A super wealthy trader with a lot of money to spend

12. Mining The process of verifying transactions on the blockchain, resulting in rewards (aka coins) for those who lend their computing power

13. Long A decision to hold a coin for the long term

14. REKT When a coin goes down sharply and you have a bad loss

15. Lambo The car that many people want to buy when they strike it rich

 

16. Swing When the price of a coin is moving up and down at a rapid rate

17. Pumping A coordinated effort to boost a coin by buying a lot of it all at once

18. Bearish When the sentiment on a coin is negative

19. Bullish When the sentiment on a coin is positive

20. Exchange Websites that allow you to purchase and sell cryptocurrencies

 

21. FIAT Any currency that is issued by a government

22. TA Technical analysis

23. ATH All-time high

24. FA Fundamental analysis

25. MCAP  Market capitalization

26. ASHDRAKED A situation where you lost all your money.

27. BTFD Buy The Fucking Dip (an indication to buy a coin when it has dumped so hard)

28. DILDO Long green or red candles

29. DUMP To Sell off a coin.

30. SAJ CANDLE  Huge green candle

 

31. SHORT Margin bear position

32. SWING  Zig zag price movement (Upwards and downwards)

33. REVERSE INDICATOR Someone who is always wrong predicting price movements.

34. RSI Relative Strength Index

Leave a Reply

Your email address will not be published.