Me ne ne Cryptocurrencies

 

ME NENE CRYPTOCURRENCY ?

Cryptocurrency na dauke da kalmomi guda biyu wanda aka dunkule su a matsayin kalma daya watau, ‘crypto’ da ‘currency’

CRYPTO: An samo ta ne daga yaren ‘Greek’ wanda tana nufin “boyayyen abu”

CURRENCY: Asalin wannan Kalmar an samo ta ne daga yaren Latin wanda tana dauke da ma’anoni guda uku (3)

1-Abinda ake amfani da shi wajen saye da sayarwa; kudi.

-Abinda mutane suka yarda da shi.

-Gaskataccen abu mai mahimmanci da labarinsa, aikinsa ko tasirinsa yake yaduwa a cikin mutane.

Daga ma’anonin nan zamu fahimci Kalmar cryptocurrency kalma ce guda biyu da suka hadu don su bada ma’ana daya, kowacce kalma ta fito daga yare daban wanda idan an hade su domin bada kalma daya to kalmar na nufin “Boyayyun kudin gaske wanda al’ummah suka yarda dasu wajen saye da sayarwa da tasirinsu yake yaduwa a cikin al’ummah”.

Koyaya dai, wannan fassara ce ta kalma amma zata iya zama matashiya ga mai karatu don ya fahimci zahirin ma’anarta dalla-dalla.

CRYPTOCURRENCY: Na’ui ne na kudaden digital da ake amfani da su wajen musayar kudi ko cinikayya a Internet wadanda aka gina akan doron fasahar blockchain. Wannan na nufin, cryptocurrency sun bambanta da sauran kudaden digital dake gudana karkashin ikon cibiyoyin kudade da gwamnati. Kafin a kira wani nau’in kudi da sunan cryptocurrency dole sai ya cika wannan sharuɗɗan:

DIGITAL: Cryptocurrency suna wanzuwa ne kawai acikin computer, babu tsabar kudinsu sannan babu takardun kudinsu, babu wani banki da ake ajiyarsu ko wata hukuma dake kula da su.

DECENTRALIZED: Cryptocurrencies kudade ne masu zaman kansu, wanda basa bukatar hukuma ko cibiyoyin kudade su jagoranci mu’amalola da su. Babu wani rumbun ajiye bayanai na wata hukuma dake aje bayanan masu mallakar cryptocurrency ko kuma bayanan mu’amalolin da aka yi da su, kamar yadda bankuna ke aje bayanan mu’amalolin da aka yi da kudaden gargajiya.

PEER-TO-PEER : Yayin tura kudaden cryptocurrency, dolane su zama zaka iya tura su kai tsaye zuwa asusun wani batare da kayi amfani da banki ba. Ko ina kake a fadin duniya ya kasance wanda zaka turawa da kai da zaka tura kudin zaku yi mu’amalar ne ba tare da amfani da banki ba.

PSEUDONYMS: Dolane cryptocurrency su zama zaka iya tura su batare da amfani da bayananka ba wanda ya hada da suna, adreshi, jinsi da dukkanin bayanan da suka shafe ka ba. Hakan na nufin zaka iya tura su batare da an san waye ya tura kudin ba.

TRUSTLESS: Dolane cryptocurrency su zama yayin amfani da su baka bukatar yarda da tsarin wata hukuma, kamar yadda yardar mu akan kudaden gaskiya sun dogara ne ga gwamnati da cibiyoyin kudade.

ENCRYPTED: Dole Cryptocurrencies su kasance Boyayyu ne cikin tsaro mai aminci, mai amfani da su ya kasance yana da lambobin sirrin da zai shigar kafin yayi amfani da su ta yadda wani ba zai iya satar kudinsa ba.

GLOBAL: kowacce kasa tana da irin kudinta na gargajiya (Fiat money) wanda kafin amfani da irin kudin a wata Kasar daban dole akwai bukatar yin chanji. Cryptocurrency wajibi ne su zama kudaden da za’a iya amfani da su a kowacce kasa dake fadin duniya.

Wadannan sune sharuɗɗan da sai kudi ya cika su sannan za’a iya kiransa da cryptocurrency. Koda kudi ana kiransa da cryptocurrency matukar bai cika wadanda sharadodin ba to bai gama zama ingantaccen cryptocurrency ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.