Tarihi Kuɗaɗen Cryptocurrencies

Kamar yadda aka sani kalmar Crypto asalin ta kalmar Girkawa ce (Greek Word), tana nufi “Secret” ko “Hidden”, abin nufi “Sirri” ko “ɓoyayyen abu”, daga nan aka samo kalmar Crypto da ma’anar ta, dalilin da yasa aka bawa kudin internet wannan suna shine saboda yadda aka shirya tsarin kimiyyar gudanar dashi, akan wani tsari da ake ce wa “Blockchain Technology”, ko “Kimiyyar da take jere akan tsari hawa-hawa kamar bulo”.

Crypto Currency kudi ne dake kan internet, wanda aka fara mu’amala dashi daga 2009 zuwa yanzu.

Sai dai, kafin a fara wannan harkar Crypto currency a yau, tun da dadewa, wuraren 1980s, masana harkokin internet suke ganin ya dace duniya ta samar ma kanta da harkokin kudaden da ba’a iya ganin su, kuma ba’a iya taba su.

Saboda cigaba da amfani da kudaden takarda yana ‘kara karya tattallin arziki duniya.

Ta yadda gwamnatoci suke kashe kudade masu yawa wurin buga su, da kashe kudade masu yawa wurin kula dasu idan sun yage ko sun ‘koke ko sun lalace, sannan ana saurin sace su da gano inda suke da wanda yake dasu.

Wannan yana daga cikin ababen da suka sa manyan masana ganin a kawo karshen wannan matsalar.

Tun daga lokacin da aka fito da tsarin transfer din kudi ta waya, daga Account din mutum na banki zuwa wani banki masana suka tabbatar da cewa tsarin Block Chain Technology zai yi nasara.

Har wa yau, tun shekarun baya masu kokarin kwato ‘yancin ‘dan Adam suna cewa ya kamata ace a yanzu mutane sun samu “Financial Freedom” wato ” ‘Yancin gashin kai ta bangaren harkokin kudi”, ba sai sun jira wata kasa ko wata gwamnati ta amince da kudi kasa ba.

Suna cewa saka bakin gwamnati cikin harkar kudi yana danne cibagan duniya da walwalar mutane.

A shekarar 1985 wani Baturen kasar America masanin harkar internet yayi yunkurin samar kudin Intenet mai kama da Crypto Currency na yanzu, sai dai kasar Amurka ta kama shi, ta daure shi, daga bisani aka yi zargin ta hallakar dashi.

A 1997 wani dan kasar Japan ya sake irin wannan yunkurin na samar da kudin Intenet amma kasar Japan ta kama shi, haka dai abun ya cigaba da tafiya tsakanin masu neman “Financial Freedom” da gwamnatocin kasashe.

A shekara ta 2008 wani masanin harkar internet kuma dan rajin neman Financial Freedom a duniya, wanda aka ce sunan sa “Satoshi Nakamoto“, yayi nasarar kera kudin Intenet, kuma ya saka masa suna “Bitcoin”.

Bayan ya kammala aikin a 2008, sai a 2009 ya qaddamar dashi, wanda shine yayi nasara a karon farko a tarihin duniya da har aka gagara dakatar dashi.

Sai dai ance Satoshi Nakamoto ya gina aikin sa ne akan wanda ‘dan kasar Japan din nan ya faro.

Har yanzu ba’a san fuskar Satoshi Nakamoto ba, sai dai bincike ya nuna cewa suna ne irin na ‘yan kasar Japan.

Shi ya Samar da Kudin farko “Bitcoin”, an saka masa sunan ne saboda an gina lissafi na’urar juyawa kudin ne da lissafin Computer na salon Algorithm, wato shi Algorithm asalin wanda ya kirkiro wannan lissafin da Computer take kai wani babban Malamin Musulunci ne, sunan sa “Imam Jabir Bin Hayyan Al-Khawarizmi”, shine Turawa suka boye sunan sa domin kada duniya tasan Musulmi ne suka kawo wannan tsarin lissafin na Computer.

Tsarin lissafin algorithm akan Computer yana bugawa ne da ‘digo ko “Bit”.

Toh daga nan suka saka sunan kudin Crypto currency na farko da “Bitcoin”, shi Bitcoin a Ranar (08-03-2021) yana Naira miliyan 25,000,000 a kudin Nigeriya.

Amma a farkon lokacin da aka kirkiro sa a 2009 bashi da daraja, bayan shekaru 10 ya tashi daga Naira goma ya koma Naira miliyan 24 ko wane daya, misali: wanda ya sayi Bitcoin guda dari a 2009 a yau Duk guda daya Naira Milyan 25

Bitcoin ba shi kadai ne Crypto Currency ba, shi Bitcoin ‘daya ne daga cikin kudaden Internet, shine na farko, shine babba dan haka yafi kowane Coin tsada.

Misali:

Idan aka ce maka akwai kudaden Takarda a duniya (Fiat Currency) a duniya da yawa, toh kudin Nigeriya (Naira) ba itace kadai kudin da ake amfani da ita a duniya ba.

Akwai Riyal, akwai Dollar, akwai Cefa, akwai Ghana Cedi, akwai Pound, akwai Yuro da sauran su.

Toh haka ma Crypto currencies suke, akwai su da yawa sun fi dubu uku akan Block Chain Technology na duniya, misali, akwai:

1. Bitcoin.2

. Etherium.

3. Litecoin.

4. Binance (BNB).

5. Doge coins.

6. Tron (TRX).

7. ADA, Cardano.

8. Steem, Hive, XRP, HOT, Smartkey da CLASSIC COIN

Leave a Reply

Your email address will not be published.