China na son murƙushe Kasuwancin Crypto

 


China na son murƙushe Kasuwancin Crypto


Babban bankin China ya ce ya kira wasu manyan bankuna da kamfanonin hada-hadar kudi don tursasa su su durkusar da kasuwancin kudin Crypto.


Babban Bankin ya ce cukumurɗar da ke cikin harkar kudin Internet na barazana ga mu’amalar kudi da kuma ba da damar halatta kuɗin haram.


Hudu daga cikin kamfanonin da aka gayyata sun ce za su yi biyayya.


Darajar kudin ta fadi kasa wanwar da fiye da kashi goma a cikin 100 a ranar Litinin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.