Bambanci tsakanin Coin da Token a harkar CryptoCurrency

 


Bambanci tsakanin Coin da Token a harkar CryptoCurrency.


Coin kudin internet ne da yake da Network nasa na kansa, Shi kuma Token kuɗin internet ne da bashi da Network nasa, sai dai an Ɗora shi akan network din wani coin.

Misalin Coins:

Bitcoin, Ethereum, LTC, XRP, Tron-TRX, BNB (Binance Coin), Fil, Solana da sauransu.


Misalin Tokens:

BTT (BitTorrent), Dent, SafeMoon, FEG, SafeMoon Cash, Pitbull, Shiba Inu (SHIB), Classic coin da saurasu.


An fara Dora Tokens akan Ethereum BlockChain, wanda suka fara samar da Smart Contract, dan haka yawancin Coins a yanzu sun faro ne daga kan Ethereum BlockChain.

Kafin Ethereum ba’a san a dora wani token akan Network na wani coin ba.


Abinda yasa Tokens suka yi yawa a yanzu shine saboda Binance Smart Chain yana da saukin transaction charges.


Abinda yasa yanzu ba’a kirkiro Tokens da yawa akan Ethereum saboda Ethereum yana da tsadar gas fee, amma gaskiya Ethereum yafi Network mai karfi da kuma tsaro.


Sannan kuma akwai Tokens din da zaka ga suna kan Network guda biyu misali sune Shiba Inu da FEG da Classic coin.

Suna kan Binance BlockChain da Ethereum Network, ko akan Exchangers zaka ga suna nuna maka, zaka ga Shiba ERC-20, Shiba BSC.


Idan kaje kan Trust wallet dinka idan ka danna kan Bitcoin zaka ga an rubuta Coin daga hannun hagu, wannan yana nuna maka shi Coin ne ba Token ba.


Ko kuma ka bude kan SafeMoon dinka a Trust wallet, daga hannun hagu a sama za kaga an rubuta Token, ko kaga BEP20, hakan yana nuna maka Token ne, amma akan Binance Network.


Manyan institutional investors sun fi so suga an gina Token akan Ethereum Network, kafin su zuba kudin su, saboda Ethereum yafi nagarta, sai dai tsada, shiyasa talakawa basa harka da Tokens din ke Kan Ethereum sosai.

Kuma zaka ga Tokens da suke kan Ethereum basa muguwar karyewa kamar yadda wadanda suke kan BSC suke karyewa da sauri.


Wani abinda zai baka mamaki wanda ya kirkiro Eithereum sunan sa Vitalik har yanzu bai kai shekaru 28 a duniya da haihuwa ba, bayan Bitcoin babu wani coin a duniya kamar Ethereum.


Coins ana iya amfani dasu akan abubuwa da dama, amma tokens ba komai ake iya yi dasu ba, musamman abinda ya shafi Payment, akwai Network din da baya karban Token sai Coin, akwai wanda kuma yake karba duka biyun.


Token yana iya komawa ya zama Coin, idan wadanda suka kirkiro shi sun samar masa da BlockChain mai zaman kansa, misali SafeMoon da Classic coin suna kokarin samar da BlockChain na tokens dinsu, daga lokacin da suka samar to shike nan ya tashi daga matsayin Token ya koma Coin, kuma zai iya karban Smart Contract da sauran su.


Wasu Token din za kaga an kirkire su ne akan Ethereum BlockChain, sune zaka ga an rubuta ERC-20 a jikin su.


Wasu Token din kuma an kirkire su akan BSC ne, wato Binance Smart Chain, sune za kaga an rubuta BEP-20.


Wasu kuma an kirkire su ne akan Tron BlockChain, sune zaka ga an rubuta TRC-20.

Wadannan sanannu kenan daga ciki.


Coin ne kawai ake iya dora masa wani Token akan sa, amma ba’a iya dora Coin akan Token.


Token basa iya karbar ayyukan tsara wasu coin akan Manhajar su, abinda suke ce ma CTN, amma Coin zai iya wannan aikin.


Akwai banbance-banbance masu yawa tsakanin Coins da Tokens, wadannan kadan ne daga ciki.

By Brr abdulhadi Isa Ibrahim

Leave a Reply

Your email address will not be published.