BINANCE DA HOUBI SUN DAKATAR DA MUTANAN CHINA KASUWANCIN CRYPTO

BINANCE DA HOUBI SUN DAKATAR DA MUTANAN CHINA KASUWANCIN CRYPTO.

Babbar kasuwar crypto currency ta Houbi ta fitar da sanarwar fara cire mutanen kasar China daga cikin kasuwarta wanda zuwa karshen shekarar nan zata kammala hakan.

Zuwa ranar 31 ga Disambar 2021 zata kammala hakan, biyo bayan matsa lamba da kasar China take yiwa kasuwar Crypto da kuma Yan crypto din dake ƙasar ko kuma suke haifaffun kasar.

Sannan itama kasuwar Binance ta daina barin dukkanin mutanen dake ƙasar China shiga cikin ta domin yin rijista – 8BTCNews

Colin Wu marubucin kafafen sadarwa kuma ɗan Crypto dake ƙasar China ya bayyana irin yadda gwamnatin kasar Sin take matsawa kamfanonin tare da hura musu wutar gallaza wa sai sun rufe hada-hadar Kasuwancin Crypto daga kasar su da rufe shafin kasuwar.

bankin People’s Bank Of China (PBOC) ya fadi na cewa sai sun fitar da kasuwar Crypto daga kasar su ko ana ha maza ha mata

Dukkan kasuwannin guda biyu wato Binance da Houbi yan asalin ƙasar China ne to amma irin wutar gaba da gwamnatin kasar take hura masu tun a shekarar 2017 na soke hada-hadar Kasuwancin Crypto acikin kasar yasa dole sai da sukayi hijira suka koma wasu ƙasashen domin kafa turakun su na cigaba da wanzuwa.

Yanzu Indai kai dan China ne ko kuma kana zaune a kasar China to muddin zakai kasuwancin Crypto sai dai kayi amfani da VPN.

Translated by
Mustapha Gfatu

Leave a Reply

Your email address will not be published.