CHINA TAYI ANIYAR RUSA KASUWANCIN CRYPTO

KASAR CHINA TA SAKE LASAR TAKOBIN HANA KASUWANCIN CRYPTO.

A ranar juma’ar Babban bankin kasar China (PBOC) ya fitar da sanarwar cewa dukkanin wasu abubuwa da suka danganci harkokin Crypto ababen laifi ne, sannan ya Shawarci gwamnatin kasar lallai ta tashi tsaye domin ganin cewa ta kawar da abubuwan dake tattare da harkar Crypto domin kare kuɗin kasar (Yuan¥).

A cikin ƙunshin sanarwar sun bada umarnin cewa dukkanin wasu kamfanoni dake rike da Manhajojin Kasuwancin Crypto (Exchangers) an basu umarnin cewa da su gaggauta rufewa ko sauke Manhajojin daga aiki, Domin hana kuɗaɗen Crypto zagayawa a kasuwa.

Wannan shine karo na uku cikin shekara daya da CHINA ta sake jaddada HARAMCIN CRYPTOCURRENCY inda ta sake daukan KWARARAN MATAKAI, tace ba ga yan cikin kasarta kawai ba, tace zata yanke Hulda da Duk wata kasa da Bata dauki kwararan matakan murkushe kasuwancin crypto ba

Bayan fitar da wannan sanarwa jim kaɗan farashin Bitcoin ya sauka da kashi biyar (5%) inda ya dawo $42,810

Bankin na PBOC ya kara da cewa yasha alwashin hatta wadanda ma suke kasashen waje Indai za suyi mu’amalar kasuwanci da yan kasar ba su isa suyi amfani da Crypto ba. Wannan shine dalilin daya janyo kasuwar Bitcoin ta sake faɗuwa a duniya, sakamakon wannan FUD din da bankin PBOC ya yayata.

Mutane sun san wannan sanarwar da gangan akayi ta domin a tada hankalin Investors da haifar musu razana ta karya, domin sanarwar da aka saka tsohuwar magana ce wacce suka fara fitar wa a kwanakin baya lokacin da zasu kori miners din Bitcoin daga ƙasar.

Ina Siyar DATAR MTN Wadda take yin wata daya 1GB akan 350 me Bukata yamin Magana a 08122225296

Zuwa Yanzu, babu wani binciken daya tabbatar da musabbabin faruwar wannan al’amari, domin wasu suna ganin ko za’a yi amfani da wannan damar ne wajen dumping sannan kuma wasu again su sake kwasar kaya a araha?

Ana zargin wannan mulkin gurguzun na kasar China Ba zai amfana mata da komai ba a wannan bangaren domin ba yau ta fara ire-iren waɗannan maganganun ba akan Bitcoin da Crypto, domin ta yi irin su a shekarar 2013, 2014, 2015, 2016, 2017, 2018, 2019, 2020, 2021 to menene kuma sabo, badi ma 2022 sai sunce sun hana kuma ba za’a daina ba.

Ko yaushe zata daina Ire-iren wadannan kare-rayi da lashe lashe takobin kuma oho!

Source:
Mustapha Gfatu and Gonar Bitcoin

Leave a Reply

Your email address will not be published.