YADDA AKE TSARA KASUWANCIN CRYPTO

Mirman Eugene dan kasar Rasha a Cikin littafin sa The Will to Whatevs yace abubuwa koda yaushe zasu iya canzawa, dan haka dan crypto bai kamata ya tsaya akan Project guda daya ya zuba kuɗi aciki ba, Musammam a lokacin da ake yawan samun consolidation a Kasuwar Crypto, Ana bukatar “Diversification of Portfolio” Raba kafa wajen zuba hannun jari, da tsara yadda zaka zuba kuɗaɗen ka cikin Crypto, Sannan ka binciki ire-iren Projects din da zaka siya.

Akwai rabe-raben bangarorin Projects a crypto Wanda kowane Coins ko Tokens yana cikin su, wannan bangarorin sune:
1) BTC + Large Caps. Alt. 50%.
2) Meme Tokens 10%
3) Stablecoin 15%
4) Mid. Caps. DEFIs 25%
Idan muka hada lissafin 50+10+15+25 = 100%

1. BTC + Large Caps. Altcoin: Sune Kashin farko wanda ake so wanda zai saka kuɗin sa ya raba su gida biyu ya saka kashi daya anan. Ba lallai sai Bitcoin ba, akwai irinsu ETH, BNB, Fil, Sol, ADA, KCS, HT, LTC, MATIC da sauransu

2. Meme Tokens: sune Kashi na biyu, Mutum Zai iya ware kashi goma na sauran rabin kudin sa ya zuba su anan, su basa bukatar shiga da manyan kudade, domin su $10 ya ishe ka ka shiga wani Projects din cikin meme ko Shitcoin ya baka dubunnan kudade. Sune irinsu Shiba Inu, Freecoin, Goat, Ukulu, Safemoon, da dai sauransu.

3. Stablecoin: Wannan shine Kashi na Uku wanda ake so mutum ya ware akalla kashi 15% na Jumullar kuɗin sa. Amfanin haka shine koda Sabon Project ya fito ko kuma ka ga wani token, cikin gaggawa zaka saye shi to kana da ragowar kuɗin da zaka iya shiga ba sai ka bukaci kudi daga waje ba ma’ana ba sai ka sake shigar da wasu. Ire-iren stablecoin din da ake saye sune USDT, BUSD da.s.s.

4. Mid-caps DEFIs: Wannan shine Kashi na hudu wanda ake so mutum ya saka kashi ashirin da biyar na Jimillar kuɗin da zai saka a Crypto business din sa. Mid-caps Decentralized Finance sune Projects din da ake amfani da su domin sarrafa wata Manhaja ko Manhajojin da ke kan Blockchain, kuma mafi yawancin su suna kan Ethereum Blockchain. Ire-iren su sune Chainlink, Pancakeswape, Uniswap, Fantom, Folkstarter da dai sauransu.

Amfanin raba kafa na cigaba da amfanar mai yin ta ne musamman idan yanayin kasuwar Crypto ya juya, idan na wancan ɓangaren basu baka riba ba to wadanda suke a ɓangare kasa zasu baka riba. Bana goyon bayan naga mutum ya zuba dukkanin kuɗin sa a rukuni guda, lallai a raba kafa.

Akwai lokacin da (Bitcoin da Altcoin mai Caps. Sosai) suka kwanta dama ko motsa wa basa yi, amma kuma Meme Tokens (Shitcoins) suna ta bada kuɗaɗe (Riba) ga wadanda suke rike dasu ko kuma suke sayen su, haka kuma munga ko a lokacin dip masu rike da DEFIs Projects suma basu sha wahalar kasuwa sosai ba domin sun zama Prime mover na saye da sayarwa.

Source : Mustapha Gfatu

Leave a Reply

Your email address will not be published.