ABINDA YA KAMATA KA SANI AKAN NON-FUNGIBLE TOKENS (NFTs)

ABINDA YA KAMATA KA SANI AKAN NON-FUNGIBLE TOKENS (NFTs)
Kana zane (Artist) amma baka Siyar da Aikin da ka zana a NFTs, wajen rage gumin wahala, to ba shakka miliyoyin kudade na wuce ka. Haka O. Daniel Yace. Cigaban da fasahar Blockchain ta kawo bawai a iyaka Kasuwancin Crypto bane da tsara cigaban harkokin kasuwanci zuwa fasahar zamani, ciki harda tsaftace yanayin gudanar da ayyuka masu yawa, abun bai tsaya iya ka nan ba, zuwa yanzu ta sake baiwa mutane dama tare da bude masu wani sabon shafi na cigaban rayuwar su, wato so nake nace a karkashin wannan fasa ta NFT mutum zai iya sayar da wani abu mallakin sa wato kana iya sayarwa da daraja kuma a siya kaima ka siya irin ta hannun Wani.

MENENE NON-FUNGIBLE TOKENS?
Asalin Kalmomin guda biyu ne aka cure su waje daya wato “Non” da kuma “fungible” suka bada abu daya wato “non-fungible” idan kuma zamu alakanta su da Blockchain ko kuma cryptocurrency sai muce “Non-fungible Tokens” wannan shine asalin Kalmomin sannan sai mu dubu ainihin ma’anar kalmomin da kuma dunkulewar su.

Kalmar “Fungible” na nufin dukkanin wani abu da za’a iya sauya shi da wani abu kwatankwacin darajar wannan abun, su kuma non-fungible na nufin wani abu da ba’a sauya shi ko canza shi kwatankwacin irin wannan, idan ma za’a sauya to hakan yana da wahala, wato kamar soyayya, ko wata waƙa ta wani mawaki ko wani zane na wani mutum da akayi masa ko wani gida daka mallaka ko kuma wani abu dai da mutum ya mallaka da shi kadai ne keda iko akan sa.

To a Bangaren fasahar kasuwanci da Cryptocurrency kuma zamu iya cewa non-fungible tokens na nufin wasu kadarori na internet (digital asset) wadanda suke da waccan halayyar irin ta non-fungibility (wato basa da makwafi) amma kuma za’a iya sayen su kuma a Siyar dasu, kamar kowacce kadara da take a zahiri. Kari akan haka shine NFTs na nufin wani wani hatimi na kadarar zahiri ko kuma badini da yake a Internet, wanda idan mutum ya sayi wannan hatimin to ya sayi waccan kadara da take a zahiri, sannan kuma idan ma ya sayar to shima wanda ya saya yana da yakinin cewa ya sayi wata kadara ne ta zahiri ko badinin.

Kwakkwaran misalai akan fungible tokens da kuma non-fungible tokens shi ne: Bitcoin guda daya farashin sa shine $60K (1 BTC = $60,000), Sannan kuma itama Dalar idan kana da $60,000 zaka iya sayen Bitcoin guda daya ($60,000 = 1 BTC) wannan shine Misalin fungible tokens.

Sannan Kuma, yanzu idan Nura M. Inuwa ya rera waka to a duniya shi kaɗai ne mai wannan wakar domin shine yayi kuma Muryar sa ce, wannan na nufin duk duniya babu mai ita sai shi to wannan kadarar sa ce kuma shine keda hakki wajen saka mata farashin daya ga dama. Wannan wakar ta zama non-fungible object a duniya.

ASALI BIJIROWAR NFTs.
Asalin bijirowar NFTs shine a shekarar 2012-2013 an samu fitowar wani Coin mai suna Colored Coins Wanda an samar dashi ne akan Blockchain din Bitcoin, wannan yasa aka dauke shi a matsayin NFT, wanda za’a iya amfani dashi wajen maye gurbin kadarar zahiri, tun daga gidaje, motoci, kanfanoni, da dai sauran kadarorin da dan adam yake mallaka.

Bayan wasu shekaru, wasu sun dukufa wajen ganin sun Inganta NFTs har zuwa shekarar 2018 zuwa 2021 wanda a wannan dan tsakanin ne aka samu bindigar bayyanar NFTs da kuma gudanar da Kasuwancin su.

Daga nan shugaban kamfanin Twitter Jack Dorsey Shima ya Shigo ɓangaren inda ya dora Posting din sa na farko a twitter da yayi a 2016 kuma ya sayar da shi a matsayin NFT, posting din duka bai wuce layi daya ba gashi kamar haka “just setting up my twttr” ya siyar dashi Dala Miliyan biyu da ɗigo tara ($2.9 Million).

INA SIYAR DA DATAR MTN DA KE YIN WATA ƊAYA, 1GB AKAN 350 mai buƙata yamin magana 08122225296

SHIN ZAKA IYA SAYE KO SAYAR DA NFTs?
Amsar ita ce, eh! Kamar yanda Cryptocurrency take da kasuwanni wato (Exchange Application) to suma non-fungible tokens (NFTs) suna da guri ko kasuwar da zaka je ka siya ko ka siyar dasu daga cikin ire-iren waɗannan kasuwannin da ake siye ko sayar da NFTs sune:
• Opensea
• Rarible
• Foundation
• AtomicMarket d.s.s
Dukkanin wadannan dama wadanda ban lissafa ba, kasuwanni ne da zaka iya zuwa ka dora NFT din ka ko saya a can. Kafin ka dora NFT din ka shafin ya shiga kasuwa akwai hatimi da zaka yi masa wanda wannan shine zai tabbatar masa da waccan dabi’ar ta non-fungibility, saboda haka duk wanda ya saya to ya sayi wannan kadarar kuma ikon ta ya bar hannun ka.

Idan Mutum ya shiga Kasuwar NFTs ko kuma zai fara ganin cewa yaga an sayi wani hoton Gwai-Gwai a farashin dubban daloli, dole ne ya yi bincike kuma Bincike mai kyan gaske, domin a kowanne gwaigwai da ka ga an saya to akwai wani labari ko martaba ko daraja dake kunshe a tattare dashi saboda haka, akwai bukatar yin Bincike na kwakwaf (tun daga dalili, zuwa shaharar wannan abun, da kuma shin jama’a suna son sa, da dai sauransu) akai kafin ka siya.

WATA KILA ZAKAYI WANNAN TUNANIN.
Yanzu misali, Bulama Catoon ya yi zanen hoton gwaigwai din sa ya dora a facebook, bayan wasu awanni kuma yace ya wallafa shi a NFT Market da sunan zai siyar, mu kuma masu bibiyar shafin sa ai munyi Saving na wannan Hoto a wayoyin mu, to nima idan na sake ɗaukar shi naje nakai kasuwar zan siyar fa to yaya za’a Kenan?
Wannan yasa, wani ƙarfi mai cike da tsaro na fasahar Blockchain ya kara bayyana, na cewa akwai kadaici na dukiyar mai kaya kuma babu maganar Kutse acikin ta, amsar tambayar can zata zo kamar haka, Bulama dai shine mai hoto kuma shi ya riga kowa wallafa wannan hoto a kasuwar NFT Saboda haka wannan zai bashi damar cewa za’a bugawa wannan hoton daya saka hatimin “Originality” ma’ana shine na farkon duk wanda za’a sako bayan nashi to jabu ne, haka kuma duk da cewa shine ya zana hoton amma da zaka riga shi ɗorawa a kasuwar NFT to naka ne Original ko ya sako nashi daga baya to ba mai kyan bane.

DAGA KARSHE.
Zuwa yanzu Blockchain din Ethereum ne kadai yake bada damar hada-hadar Kasuwancin NFTs, ma’ana zaka siya ko ka siyarwa ne da Ethereum, amma akwai yiwuwar za’a iya samun karin wasu Blockchain din.

Gudanar da akalar siye ko sayar da NFTs dai bata wuce Demand and Supply din dake hannun mai ita, ma’ana zaka sayen NFT idan ka samu mai saye ka sayar masa, idan ma abin da ka siya yana da farin jini mutanen da zasu saya zasu yi tururuwar saye a wajen ka sai ka zabi wanda yafi dora maka riba ka siyar.
Su dai NFTs na iya zama kadarorin zahiri ko kuma na badini (Digital), Maimakon yau ace kaje ka siyo wani hoton zane na gargajiya ko na tarihi da zaka rataye a dakin ka ko Ofis to zaka iya sayen hoton sa na NFTs muddin an kaishi kasuwa za’a siyar ya zama mallakin ka a duniya

 

• Me nene Alakar NFT da kuma Coin din dake kasuwa?
Bayani: NFTs ba Normal token ne dake kasuwa ba, sai dai wadanda zasu kirkire shi sukan yi Taking advantages na wancan real NFT din sai suyi token a karkashin sa wanda zai baiwa masu sha’awar kasuwancin sa dama guda biyu, wato ma’ana, ta yiwu kana so ka siya amma sakamakon tunda akan Ethereum ake cinikayya to gas fee ya hana ka siye, amma idan akwai Normal tangible coin nashi to zaka iya zuwa ka siya, dukkanin lokacin da wancan NFT din ya samu Value shima Coin din daka siya zai samu karin wannan Value din a farashin sa.

• Menene Alaka ko kuma Ingancin Coin din da aka saka masa suna NFT kuma ba wani NFT project da aka yi Binding dashi?
Jawabi: Kasantuwar yanda Kasuwar NFTs take kara samun masu supporting wajen cigaba da trading nasu yasa wasu suke amfani da wannan Trending character din suyi Coin mai suna NFT Saboda haka wanda bai sani ba, da yaji ana ambaton irin yanda ake samun kudade da NFTs sai ya garzaya Normal Exchanger market yaje ya kwasa, hakan na iya sawa ka sayi rubabben projects da zaka iya yin asara nan gaba.

Ana samun masu kyau, amma lalle kafin ka siya kayi bincike akai sosai wajen tabbatar da ingancin sa kafin ka siya, bawai da kaga Coin ko Token mai suna NFT ka Kwashe kudin ka ka zuba ba.

• Ta yaya zan Iya Kirkiro NFT kuma na Siyar?
Amsa: Akwai manyan Manhajojin zane irin su Adobe Photoshop, Adobe Illustrator, Corel Draw, d.s.s duk zaka iya aiwatar da zanen NFT aciki, sai dai kana da bukatar kwarewa tukunna akai domin, sai ka nazarci kasuwar Sannan zaka zana abin da kasan zai janyo hankalin masu saye.

Source: Mustapha Gfatu

Leave a Reply

Your email address will not be published.